Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF) ta bayyana dalilin saukar gaggawa da jirginta ya yi a Burkina Faso yayin da yake kan hanyarsa zuwa Portugal.
A cikin sanarwar da rundunar ta fitar, an ce jirgin ya tashi daga Legas amma ya fuskanci wata matsala, wanda ya sa aka yi taka-tsan-tsan a filin jirgin sama mafi kusa.
Rundunar ta jaddada cewa matakin ya yi daidai da ƙa’idojin tsaro na jiragen sama na ƙasa da ƙasa.
“Ma’aikatan rundunar suna cikin ƙoshin lafiya kuma hukumomin da suka karɓe su sun basu kulawa ta musamman. Ana ci gaba da shirye-shiryen kammala aikin da aka sanya a gaba,” in ji sanarwar.
NAF ta gode wa tallafin da aka samu a lokacin lamarin sannan ta tabbatar wa jama’a cewa za ta ci gaba da bin ƙa’idojin aiki da na tsaro, tare da kula da lafiyar ma’aikatan ta, yayin da take kiyaye dokokin da tsarin mulki ya tanada.
Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar rashin amincewa da sauyin kawance a yankin Yammacin Afirka.
Burkina Faso, Mali da Nijar sun kafa ƙungiyar AES, lamarin da ya sa suka bar ECOWAS a farkon wannan shekarar.
