Mutane 14 da suka hada da mata da wani ƙaramin yaro sun rasu sakamakon haɗarin jirgin ruwa a yankin Gumbi da ke Karamar Hukumar Yawuri a jihar Kebbi.
Lamarin ya faru ne bayan magariba, inda irgin ruwan da ke ɗauke da mutane sama da 70 ya rabe gida biyu a hanyar sa ta dawowa daga kai amarya a yankin Karamar Hukumar Ngaski.
Alʼummar yankin sun ce wadan da suka rasun mata ne, sai kuma wani ƙaramin yaro guda ɗaya.
Masu aikin ceto sun ce sun samu nasarar ceto sauran mutanen da ke cikin jirgin, yayin da ake ci gaba da tattara bayanai kan musabbabin haɗarin.
