Ƙungiyar Kwankwasiyya ta nuna damuwa kan rahotannin da ke cewa Gwamnatin Jihar Kano na shirin ɗora wa ƙananan hukumomi 44 na jihar bashin da ya kai kusan naira biliyan 55 daga wani babban bankin kasuwanci.
Mai magana da yawun ƙungiyar, Habibu Sale Mohammed, ya ce ana zargin za a ɗora wa kowace ƙaramar hukuma nauyin bashin kusan naira biliyan 1.3.
Sanarwar ta ce ana sa ran za a yi amfani da kuɗin wajen gina cibiyoyin jarabawar kwamfuta ta CBT, da kuma shirin tallafa wa jama’a ta hanyar ba su jari.
Sai dai ƙungiyar ta ce duk da muhimmancin irin waɗannan ayyuka, ya kamata a gudanar da su cikin gaskiya, bin doka da kuma kiyaye muradun al’umma.
Sanarwar ta kuma buƙaci gwamnati ta yi cikakken bayani kan kuɗaɗen da ƙananan hukumomi suka bayar ko aka karɓa daga gare su a ƙarƙashin shirin tallafa wa mata da sauran shirye-shiryen haɗin gwiwa a baya.
