Akalla mutane 54 ne suka rasa rayukansu sakamakon cizon maciji a Jihar Gombe a shekarar 2025, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta jihar ta bayyana.
Likitan kula da yaɗuwar cututtuka na jihar, Dr. Nuhu Bile, ya bayyana hakan ne yayin taron Kwamitin Kula da Matsalolin Gaggawa na Lafiyar Jama’a da aka gudanar a Gombe ranar Talata.
Dr. Bile ya ce a bana, mutane 1,591 ne suka kai rahoton cizon maciji a Asibitin Kula da Cizon Maciji na Kaltungo, inda 54 daga cikinsu suka mutu.
Ya bayyana cewa adadin cizon maciji a bana shi ne mafi ƙanƙanta cikin shekaru huɗu, inda aka samu 2,794 a 2022 da 2,594 a 2023, da 2,189 a 2024.
Ya ƙara da cewa galibin waɗanda suka samu cizon maciji na zuwa asibiti ne kawai idan lamarin ya yi tsanani.
Game da sauran cututtuka, Dr. Bile ya ce an samu mutane 176 da suka kamu cutar kwalara a 2025, inda biyar suka mutu, yayin da aka samu Mutum 14 na zazzaɓin Lassa, inda takwas suka rasa rayukansu.
