
Ɗan takarar gwamnan Jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress ADC a zaɓen 2023, Malam Ibrahim Khalil, ya bayyana cewa jam’iyyar su na maraba da sababbin mambobin da suka shigo daga wasu jam’iyyu, musamman masu haɗakar siyasa da suka sauya sheƙa zuwa ADC.
Malam Khalil ya bayyana haka ne yayin da yake tsokaci kan sauya sheƙar wasu ’yan adawa zuwa jam’iyyarsu, inda ya bayyana hakan a matsayin ci gaba ga dimokuraɗiyyar Najeriya.
Sai dai, ya bayyana cewa duk da maraba da suke yi da sababbin mambobi, hakan ba zai hana su kare haƙƙin tsoffin mambobi ba.
Ya ce, ADC jam’iyya ce da ke bin tsarin siyasa na gaskiya da adalci, kuma tana da buƙatar hadin kai da mutunta juna domin cimma manufofin da ta sa a gaba.
Malamin ya ƙara da cewa, Siyasa ba ta daɗi idan aka fara danniya da son zuciya, ya kuma ce idan ana so a yi canji na gari, dole ne a mutunta juna.
Jawabin Malam Khalil na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun karbar sababbin mambobi daga wasu jam’iyyu zuwa ADC, lamarin da ke nuna yadda rikicin siyasa ke ƙara fadada a kasarnan, musamman a shiyyoyin da ke fama da rikice-rikicen jam’iyyu.