Sanatan Kano ta tsakiya Rufai Sani Hanga yace motoci 15 da aka bayar domin aikin jam’iyya ne kadai aka bukaci a dawo dasu domin sake baiwa yan jamiyyar da suka tsaya a NNPP, sabanin labarin kanzon kurgen da ake yadawa cewa sanatan ya nemi duk wadanda ya baiwa motoci sama da 170 su dawo da su.
Bayanin hakan ya fito ne daga kakakin sanatan Ibrahim Abdulhamid Namadobi a tattaunawarsa da Premier Radio a safiyar Talata.
Namadobi yace ya zama wajibi su wayar da kan jama’a kan wannan batu, saboda yadda wasu yan adawa ke kokarin sauya umarnin da Sanatan ya bayar da gan-gan domin su goga masa kashin kaji
“Wannan fa ba sabuwar Magana bace, kowa ya san motocin da aka bayar domin aikin jamiyya daban, wadanda aka bayar domin kyuata ta kashin kai wadanda suk hauara 170 suma daban, anan ana Magana ne kan motoci 15 da sanata ya bayar domin aikin jamiyya, sune aka ce a dawo dasu”.
Namadobi yace batun ajiye kayan aiki bayan barin office ko jamiyya ba sabon abu bane, domin ko gwaman ya fita daga office ajiye kayan gwamnati yake wadanda aka bashi domin yin aikin al’umma
“ko a gwamnati idan mutum y agama mulki ajiye kayan aiki yake ya barwa masu zuwa su dora, ba tafiya ake yi dasu ba, kowa ya san wannan, a dokar zabe wadda aka yiwa gyara, ko jamiyya cer gaba daya tace ta dai na, zata koma cikin wata jamiyyar a kai’da duk akayan aikin jamiyyar hukumar zabe ake kai mwa, hatta Biro, yakamata jama’a su gane, ba wadancan motoci da sanata ya ranba ake Magana ba, iya wadanda aka bayar don aikin jamiyya kadai aka ce a dawo dasu, kuma dama haka ake yi, tun da sun ce sun fita daga jamiyya , sai su ajiye mana kayan aikinmu” inji Namadobi
Kakakin Sanata Hangan, ya bukaci al’umma musamman wadanda suka amfana da tagomashin sanata hanga na rabon motoci, da suyi watsi da wannan labara.
Batun umarnin dawo da motocin da sanata Hanga ya raba domin aikin jamiyyar NNPP dai ya tada kura a shafukan sada zumunta, bayan Gwamna Abba Kabir Yusif ya fice daga Jamiyyar NNPP zuwa APC.
