Farashin kayan abinci na cigaba da faduwa a kasuwanni daban daban.
A wani bincike da wakiliyarmu ta gudanar ya nuna cewa farashin shinkafa ya ragu sosai a kasuwanni Kano sakamakon shigowa da ita da kuma sauran kayayyaki ta iyakoki, abin da ya jefa ’yan kasuwa da kuma manona cikin damuwa.
Rahotanni sun bayyana cewa farashin buhun shinkafa ta gida da ta waje ya faɗi warwas a kasuwanni daban daban sakamakon yawan kayan da ake shigowa da su daga waje.
Shugaban gamaiyar manoma ta kasa reshen jihar kano Abdullah Ali Mai bired, a hirarsa da wakiliyarmui ya ce, ba sa bakin ciki da saukar farashi, sai dai suna bukatar idan ya sauka kayan da suke amfani da wajen noma su ma su sauka.
“Kayan aikin da muke amfani duk sun linka kudinsu, ga Kuma iftilai na damuna da ya same mu wanda ruwa bai kai karshe ba. Wanda hakan ya sa mu ka yi asara da yawa”. In ji shi.
Daga bisani manoman sun roƙi gwamnati da ta tallafa musu domin tabbatar da daidaiton farashi.
Masana sun yi gargadin cewa faduwar farashin na iya zama na ɗan lokaci, saboda rashin tabbas a kasuwa da yiwuwar farashin ya sake hawa kafin ƙarshen shekara.
