Tsohon Babban Lauyan kasa, Abubakar Malami (SAN), ya musanta zarge-zargen da ke danganta shi da daukar nauyin ta’addanci, yana mai cewa zargin ba su da tushe kuma siyasa ce kawai ake yi da sunansa.
A wata sanarwa da ya fitar, Malami ya ce hankalinsa ya kai kan wani rubutu da ke nuni da cewa shi da wasu mutane suna da alaka da wadanda ake zargi da ta’addanci ko taimaka wa masu aikata laifin.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa tsohon ministan ya bayyana wadannan zarge-zarge a matsayin “ba su da tushe, balle makama.
Ya ce ba a taba gayyatar sa, bincike ko kuma tuhumarsa ta kowace hanya daga wata hukuma ta tsaro a cikin gida ko waje ba kan batun daukar nauyin ta’addanci.
Malami ya jaddada cewa irin wadannan rahotanni na iya bata suna da tayar da hankali, don haka akwai bukatar a yi taka-tsantsan wajen yada bayanai marasa inganci
