Majalisar dinkin duniya ta kudiri aniyar tallafawa gwamnatin Kano a bangarori da dama domin dacewa da muradun majalisar dinkin duniya masu dorewa na 2030.
Mataimakiyar shugaban majalisar dinkin duniya Hajiya Amina Muhammad ce ta bayyana hakan a wata ziyara ta musamman da ta kawo jihar Kano kuma ta gana da gwamna Abba Kabir Yusuf.
A yayin ziyarar Hajiya Amina Muhammad ta yaba da kokarin gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf abisa sauye sauyen da ya samar a jihar.
Ta Kuma shaida cewa majalisar dinkin duniya zatayi aiki da jihohin Arewacin Najeriya domin tabbatar da dorewar muradun majalisar dinkin na shekarar 2030.
Tace Kano na da mahimmaci matuka ga wannan shiri na majalisar,kuma majalisar zata duba wasu matsaloli da suke damun Arewa musamman a Kano.
Tace Kano nada matasa masu dinbin yawa da kuma nuna karewa a kirkire kirkire,sannan majalisar zata duba bangarori da suka hada da Ilimi da lafiya da noma da sauransu.
Hajiya Amina tace , Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma nuna gamsuwarsa akan wannan kudiri na majalisar ta dinkin duniya.
A shekarar 2015, ƙasashen duniya da ke cikin Majalisar Dinkin Duniya ciki harda Najeriya suka amince da manufofi 17 domin kawo ci gaba mai dorewa zuwa shekara ta 2030.
Hajiya Amina Muhammad ta kuma ce tazo Najeriya ne domin ta’aziyyar marigayi tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya rasu a ranar Lahadin da ta gabata a London.
Daga nan gwamna Yusuf ya godewa mataimakiyar Shugaban majalisar ta dinkin duniya tare da tabbatar mata da cewa gwamnatinsa a shirye take domin yin aiki tare.
