
Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya musanta iƙirarin da Shugaban Trump ya yi cewa an lalata wuraren nukiliyar Iran a hare-haren sama da Amurka ta yi a watan Yuni.
A sanarwa da aka wallafa a shafinsa na intanet, Khamenei ya fada wa Trump cewa ya ci gaba da “mafarki” kan maganganun da ya yi game da lalata wuraren.
Khamenei ya kuma tuhumi ikon Shugaban Amurka na “faɗa wa wata ƙasa abin da ya kamata ta mallaka ko kada ta mallaka idan tana da masana’antar nukiliya.”
A tsakiyar watan Yuni, Isra’ila ta ƙaddamar da wani gagarumin hari ta sama kan Iran.
Amurka ta shiga cikin wannan hari na dan lokaci, inda ta kai farmaki kan muhimman wuraren nukiliyar Iran.
A makon da ya gabata, yayin wani jawabi a majalisar Isra’ila, Trump ya sake nanata cewa Amurka ta tabbatar da “lalata” wuraren nukiliyar Iran yayin hare-haren.