Ahmad Hamisu Gwale
Tsohon dan wasan na Leicester City Musa, ya bayar da kyautar ne lokacin da ya kai ziyara masaukin ‘yan wasan a daren Juma’a.
Ahmed Musa, ba zai samu damar buga wasa ba tun bayan raunin da ya samu a kara wa da Bayelsa United.
Kano Pillars dai na shirin fafata da Abia Warriors a yau Asabar, a wasan mako na 24 a gasar Firimiyar Najeriya NFPL.
Kyaftin din din Super Eagles Ahmed Musa, ya gwangwaje ‘yan wasan ne domin karfafa musu gwiwa, a wasan da zasu karbi bakuncin Abia Warriors, a filin wasa na Sani Abacha, da ke Kofar Mata, a yau Asabar da karfe 4.
![](https://premierradio.ng/wp-content/uploads/2025/02/photo-output-13-1024x576.jpeg)