Hukumar Kwastam shiyyar Bauchi, ta ce ta kama fatar jakuna 718 da kudinsu ya haura Naira miliyan 24, da ake zargin ana kokarin fitar da su ƙetare ta haramtacciyar hanya.
Kwamandan hukumar mai kula da shiyyar Bauchi, Abdullahi Kaila ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai kan ayyukan yaki da safarar haramtattun kaya a hedikwatar hukumar da ke Bauchi.
Ya kara da cewa wannan Kaman ya yi daidai da umarnin Shugaban hukumar ta Kwastam, Bashir Adewale, na aiwatar da tsauraran matakai kan safarar dabbobi da ke fuskantar barazanar karewa.
Ya ce har yanzu kasuwanci da fitar da fatar jakuna haramun ne bisa dokokin Najeriya da kuma yarjejeniyoyin kasa da kasa, ciki har da wadda ta takaita kasuwancin dabbobin da ke fuskantar barazanar karewa.
A cewarsa, an kama mutane biyu, ciki har da direban motar da ta ɗauko kayan da kuma mai kayan, kuma za a gurfanar da su bisa dokar hukumar ta 2023 da sauran dokokin kare muhalli.
Kaila ya kara da cewa nasarar wannan aiki ta samu ne sakamakon ingantaccen hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, wanda ya inganta musayar bayanan sirri tare da tarwatsa hanyoyin masu safara a yankin.
