Kawo yanzu Kwamishinoni uku ne suka sanar da ficewarsu daga jamiyyar NNPP bayan fitar Gwamna Abba Kabir Yusuf a jiya Juma’a.
Daga cikin wadanda suka fice akwai Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dr. Dahiru Muhammad Hashim, wanda ya sanar da ficewarsa a cikin wasiƙa mai dauke da kwanan watan ranar 23 ga Janairu, 2026, da aka aika zuwa shugabancin NNPP na mazabar Gobirawa a karamar hukumar Dala.
Dr. Dahiru ya ce matakin ya samo asali ne daga kyakkyawan niyya da kuma sha’awar kawo ci gaba a Jihar Kano, tare da nuna cewa matakin ya dace da shugabanci da manufofin Gwamna Yusuf.
Shima Kwamishinan Harkokin Ruwa, Umar Haruna Doguwa ya ce ya fice daga jam’iyyar saboda rikice-rikicen shugabanci da rashin hadin kai a NNPP.
- Jam’iyyar NNPP Ta Kori Shugabanta na Kano
- Kwankwaso ya gana da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar NNPP a jihar Kuros Ribas
- Jam’iyyar NNPP ta zargi APC da kokarin tayar da rikici a Tudun Wada
A safiyar yau, kwamishinan kananan hukumomin da masarautun Kano Hon. Muhammed Tajo Othman ya sanar da fita daga jam’yyar NNPP.
Bayan kwanishinonin suma wasu shugabannin ma’aikatun gwamnati sun bi sahun gwamnan wajen fita daga jam’iyyar ta NNPP.
Daraktan Hukumar samar da Wutar Lantarki a Karkara ta Jihar Kano, Injiniya Sani Bala Iliyasu, ya sanar da ficewarsa daga NNPP a shafinsa na Facebook.
