Wani kwale-kwale dauke da fasinjojin kimanin 200 ya kife a kogin Neja.
Lamarin ya faru ne a safiyar Juma’a a yayin da kwale-kwalenke ratsa kogin daga sashen Dambo-Ebuchi na tekun Neja wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane masu yawa.
Waɗanda lamarin ya faru a gaban su sun shaida wa tashar talbijin ta Channels cewa, kwale-kwalen, mai dauke da fasinjojin na wani mai suna Musa Dangana ne, kuma cikin fasinjoji sama da 200, da ke ciki har da mata da ‘ƴankasuwa da kuma masu aikin gona waɗanda za su tafi kasuwar mako-mako ta Katcha.
A watan Oktoba ne aka samu irin wannan hatsarin a rafin Muwo Gbajibo ta ƙaramar hukumar Mokwa ta jihar ta Neja inda mutane da dama suka rasu.