Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama ta Duniya (Human Rights Commission) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sake tunani kan sabuwar dokar haraji da shugaban kasa ya mika wa majalisar kasa.
Shugaban kungiyar Kyaften Abdullahi Bakoji mai ritaya ne ya bayyana haka, yana mai cewa babban damuwar sabon tsarin harajin shine yadda zai jefa talakawan kasar nan cikin mummunan yanayi.
Ya kuma lissafa wasu illoli da sabon tsarin harajin zai yiwa wasu jihohin arewacin kasar da ma yadda za’a samu koma baya a harkar Ilimi.
Shugaban ya yi kira ga shugaban kasa da ya sake tunani kan la’akari da wadannan tsare-tsare dokar da ke fifita tara haraji kawai kan jin dadin al’umma akan.
Sannan ya ja hankalin ‘yan majalisa nan da su tabbatar da sun yi nazari mai zurfi tare da gyara kan dokokin domin tabbatar da adalci.