Kungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International, ta nemi hukumomin ƙasar nan da su gudanar da bincike kan abin da ta bayyana a matsayin amfani da ƙarfin da ya wuce kima a yayin da ake zanga-zanga a Karamar Hukumar Lamurde ta Jihar Adamawa.
Wannan na cikin wani saƙo da Amnesty International ta wallafa a shafinta na Facebook.
Gwamnati na nuna gazawa wajen kare rayukan jama’a – Amnesty International
Zanga-zangar ‘yan kwangilka ya sa Majalisar Wakilai dakatar da zamanta
Kungiyar ta ce, an samu rahoton mace-macen mata 9 a lokacin zanga-zangar, inda ta ce hakan ya biyo bayan harbin bindiga yayin da ake taron jama’a.
Amnesty ta kuma ce akwai mutane da dama da suka samu raunuka a jikinsu.
Kungiyar ta ce rikicin kabilanci tsakanin Bachama da Chobo yana kara kamari, tana mai cewa akwai bukatar hukumomi su kara azama wajen daukar mataki domin dakile tashin hankali a yankin.
Amnesty International ta nemi hukumomin tsaro su kara mayar da hankali wajen gudanar da ayyukansu cikin bin ka’idoji da kuma tabbatar da kare rayukan jama’a.
