Ƙungiyar Likitoci ta kasa rashen jihar Edo ta ce sun dakatar da aiki har sai hukumomi sun ɗauki matakin kuɓutar da wasu mambobinta biyu da ƴanbindiga suka sace a kan hanyarsu da zuwa wurin aiki a jihar.
Ƙungiyar ta ce ta ɗauki matakin ne domin ganin an kare rayukan duka sauran mambobintu da ke faɗin jihar.
- Gwamnatin tarayya za ta biya basussukan da likitoci ke bin ta
- Likitoci sun fara wani sabon yajin aikin a kasar nan
- Likitocin Idanu Na Najeriya Sun Gudanar da Babban Taro a Kano
Sakataren ƙungiyar Likitoci ta ƙasar, Dokta Mannir Bature Tsafe ya shaida wa BBC Hausa cewa bayan sace likitocin biyu, da aka yi garkuwa da su tare da ɗaya daga cikin ‘ƴan’uwansu, bayanan na cewa an ma kashe ɗan’uwan.
Dokta Mannir yace hakan yasa hankalnsu ya tashi suka dauki matakin dakatar da aiki har sai sun ga irin hoɓɓasan da jami’an tsaro za su yi don ceto mambobin nasu.
