
Aminu Abdullahi Ibrahim
Wata babbar kotu a Abuja, a Larabar nan ta soke umarnin da ta bayar na kama shugaban rikon kwarya na jam’iyyar PDP, Kabiru Turaki wanda ke adawa da tsagin ministan Abuja Nyesom Wike.
Idan za a iya tunawa a ranar 26 ga watan Maris kotu ta bayar da umarnin kama shugaban rikon kwarya na jam’iyyar PDP, Kabiru Turaki bisa kin bayyana a gabanta.
Mai shari’a Peter Kekemeke ne ya janye umarnin biyo bayan rokon da lauyan Turaki mai suna Chris Uche SAN yayi a gaban kotun.
Haka kuma ya nemi afuwar kotun bisa Rashin bayyana a gabanta a ranar da aka sanya wacce ta gabata.
Mai shari’a Peter Kekemeke, ya dage cigaba da sauraron karar babban sufeton ‘yan sanda na kasa ya shigar da shi zuwa 22 ga watan Afirilu.
