Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 26 ga Fabrairu, 2026 domin yanke hukunci a shari’ar da Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta shigar kan DCP Abba Kyari, wanda aka dakatar.
NDLEA na tuhumar Abba Kyari, tsohon Shugaban Rundunar ’Yan Sanda Masu Yaƙi da Garkuwa d a Mutane (IRT), tare da ’yan uwansa biyu kan zargin rashin bayyana kadarorinsu.
A ranar Juma’a Mai shari’a James Omotosho ya sanya ranar, bayan lauyoyin NDLEA, Sunday Joseph; lauyan Abba Kyari, Onyechi Ikpeazu, SAN; da lauyan ’yan uwansa, Monjok Agom, sun gabatar da hujjoji da muhawara kan tuhumar.
- Tinubu Ya Sake Nada Buba Marwa A Matsayin Shugaban NDLEA
- Gwamnan Kano Abba Kabir ya sanya hannu kan dokar kafa kwalejin fasaha a Gaya.
- NDLEA Tace An Samu Raguwar Shaye-Shaye A Kano
A cikin tuhumar da ta ƙunshi laifuffuka 23, NDLEA ta ce ta gano kadarori 14, ciki har da manyan shaguna, gidaje, filin wasan polo, filaye da gonaki mallakar Abba Kyari, a Birnin Tarayya Abuja da Maiduguri a Jihar Borno.
NDLEA ta kara da cewa ta gano sama da Naira miliyan 207 da kuma Yuro 17,598 a asusun bankunan Abba Kyari daban-daban.
Sai dai Abba Kyari, ya dage cewa ya bayyana kadarorinsa da na matarsa bisa ƙa’ida, ya kuma musanta mallakar wasu kadarorin da NDLEA ta danganta masa, inda ya bayyana cewa wasu daga cikin kadarorin na mahaifinsa ne da ya rasu, wanda ya bar ’ya’ya kusan 30.
