Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa ta Jihar Kano (KNCDC) ta gana da shugabannin Jami’ar Khalifa Isiyaka Rabi’u da ke Kano domin tattaunawa kan samar da jami’in kula da cututtuka a harabar jami’ar.
Ziyarar ta gudana ne a ranar Laraba, inda jami’an hukumar suka duba wasu dalibai biyar tare da ba wa wadanda ke nuna alamun cutar mashako magunguna.
Babban Daraktan KNCDC, Farfesa Muhammad Adamu Abbas, ya bayyana cewa hukumar tare da shugabancin jami’ar sun amince da samar da wakilin kula da cututtuka daga cikin jami’ar, wanda zai rika sanar da hukumar duk wata alamar barkewar cuta domin daukar mataki cikin gaggawa.
Ya ce aikin hukumar shi ne dakile cututtuka masu yaduwa tun kafin su kai matakin annoba, inda ya jaddada cewa tsarin samar da wakilai zai taimaka wajen hanzarta daukar matakan kariya.
“Bayan makarantu, za mu fadada wannan shiri zuwa kasuwanni da tashoshin mota, inda za a samar da wakilai da za su taimaka wajen gano da dakile cututtuka masu yaduwa,” in ji Daraktan.
Hukumar ta yi kira ga al’umma da su kasance masu kula da lafiyarsu, su rika zuwa asibiti da wuri idan sun lura da alamun rashin lafiya, tare da bayar da hadin kai ga jami’an lafiya domin dakile yaduwar cututtuka a cikin al’umma.
