Rundunar ‘yan sandan ta Kasa ta tabbatar da sace ɗan majalisa Samaila Bagudo a gidansa inda ta ce ‘yan bindiga ɗauke da makamai sun afka gidan ɗan majalisar da ke Ƙaramar Hukumar Bagudo inda suka sace shi jim kaɗan bayan ya kammala Sallar Isha’i yana hanyarsa ta komawa gida.
‘Yan sandan sun ce tuni aka aika da jami’an tsaro domin ƙoƙarin ceto ɗan majalisar.
A cewar sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Nafiu Abubakar, ya fitar ya ce An tura tawagar hadin gwiwa da ta ƙunshi ‘yan sanda, sojoji, da ‘yan sa kai zuwa yankin domin aikin ceto.
- Gwamnan Jihar Kebbi ya bawa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30
- Yan Daba sun kai wa Tawagar tsohon Ministan Shari’a Hari a Birnin Kebbi
Sanarwar ta ƙara da cewa kwamishinan ‘yan Sanda ya sake tabbatar da kudirin rundunar wajen kare rayuka da dukiyoyi a fadin Jihar Kebbi, yana bayyana garkuwar a matsayin “mummunan aiki da ba za a bar shi haka kawai ba.”
Rundunar ta kuma roƙi jama’ar jihar da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu kula, tare da bayar da bayanai masu amfani da za su taimaka wajen aikin ceto da ke gudana.
