Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Ƙasa (NCAA) ta bayyana cewa duk da ana sayar da tikitin jiragen sama kusan miliyan 14 a duk shekara domin zirga-zirgar cikin gida, adadin ƴan Najeriya da ke amfani da jirgin sama akai-akai bai kai mutum miliyan ɗaya ba.
Daraktan Kula da Ingancin Jiragen Sama na NCAA, Godwin Balang, ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi kan halin da fannin sufurin jiragen sama ke ciki.
A cewarsa, yawan tikitin da ake sayarwa ba yana nufin mutane miliyan 14 ne ke hawa jirgi ba, domin mutum guda na iya sayen tikiti sau da dama a cikin shekara saboda yawan tafiye-tafiyensa.
Balang ya ce wannan na nuna cewa har yanzu jirgin sama bai zama hanyar sufuri da mafi yawan ƴan Najeriya ke amfani da ita ba.
Ya kuma jaddada bukatar rage tsadar tikitin jiragen sama da inganta ayyukan kamfanonin sufurin jiragen sama domin ƙara jawo matafiya da bunƙasa fannin.
