Jam’iyyar NNPP ta bayyana takaicinta kan ficewar gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, daga cikinta, inda ta bayyana matakin a matsayin cin amanar da al’ummar Kano suka ba shi.
A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Ladipo Johnson, ya fitar a ranar Juma’a, NNPP ta ce an zaɓi gwamna Abba Yusuf ne bisa dogon alaƙarsa da tafiyar Kwankwasiyya da kuma amincewar jama’ar jihar Kano, ba wai don kansa kaɗai ba.
- Kwamishinoni 3 sun fice daga jam’iyyar NNPP
- Kwankwaso ya gana da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar NNPP a jihar Kuros Ribas
Jam’iyyar ta ƙi amincewa da hujjar da gwamnan ya bayar cewa ya fice ne saboda rikicin da ba shi da mafita a cikinta, inda ta bayyana wannan ikirari a matsayin marar tushe kuma wani abu da aka ƙirƙira daga baya domin neman uzuri.
