Kungiyar kare hakkin ɗan adam ta Amnesty International ta yi tir da mummunan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai kan masu masallata a Katsina.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, kungiyar ta bukaci gwamnati ta ƙara tsananta matakan tsaro da kuma nemo adalci ga waɗanda abin ya shafa.
‘Yan bindigan sun kai harin ne kan wasu masallata a kauyen Na’alma, cikin Karamar Hukumar Malumfashi, Jihar Katsina, a lokacin sallar asuba.
Rahotanni sun nuna cewa, har yanzu ba a tabbatar da adadin mutanen da suka mutu ba, domin wasu da dama da suka yi ƙoƙarin tserewa daga wurin harin ba a gano su ba tukuna.
Haka kuma, wasu da suka ji rauni sosai na karɓar magani a asibitoci daban-daban a yankin.
Harin na zuwa kimanin watanni biyu bayan makamancinsa a Unguwan Mantau, inda ‘yan bindiga suka kashe mutane fiye da 50 a cikin karamar hukumar ta Malumfashi.
