
Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta ware kashi 28 cikin 100 na kasafin kudin shekarar 2027 ga bangaren ilimi, wanda ya kai naira tiriliyan daya da biliyan 107 baki daya.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2027 a gaban majalisar dokokin jihar.
Gwamnan ya ce bangaren ilimi ne zai fi samun kaso mafi yawa a cikin kasafin, wanda ya ce an tsara shi ne domin inganta harkokin ilimi da bunkasa jarin dan Adam a jihar.
Ya bayyana cewa gwamnatin ta dauki malamai dubu 8 da 588 aiki a shekarar kasafin kudi ta 2026, ciki har da malamai dubu 4 da 900 na dindindin da kuma wasu dubu 3 da 688 karkashin shirin BESDA.
Haka kuma, gwamnatin ta biya kudaden jarabawar NECO, NBAIS da NABTEB na dalibai sama da dubu 150, tare da biyan basussukan ciyar da daliban makarantun kwana da kuma gyaran wasu cibiyoyin ilimi.
Gwamna Abba Yusuf ya kara da cewa gwamnatin ta taimaka wa dalibai wajen rajistar jarabawar shiga jami’a ta JAMB, tare da samar musu da horon shirin jarabawa. Ya kuma ce Kano ta ci gaba da kasancewa kan gaba a jadawalin sakamakon jarabawar NECO ta shekarar 2026 a karo na biyu a jere.
Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da zuba jari wajen horar da malamai, gyaran makarantu, samar da kayan koyarwa da kuma inganta amfani da fasahar zamani a harkokin ilimi.
