Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta ce ta kama mutane 9 da ake zargi da hannu a kisan kai da rikicin da ya barke a kasuwar Gujungu da ke karamar hukumar Taura, tare da kwato shanu 6.
Mai magana da yawun rundunar SP Lawan Shiisu Adam ya ce an kama wani matashi mai suna Saminu Ibrahim mai shekaru 20 bisa zargin kashe wani takwaransa bayan takaddamar da ta rikide zuwa fada a kauyen Dabigel da ke karamar hukumar Ringim.
Haka kuma, rundunar ta ce ta kama wasu mutane 2 da ake zargi da kai hari ofishin ’yan sanda da kona rumfuna a kasuwar Gujungu, bayan rikicin da ya biyo bayan takaddama tsakanin wani soja da wani matashi mai suna Biniya Alhaji Ibrahim wanda daga bisani ya rasu sakamakon raunukan da ya samu.
Rundunar ta ce tana ci gaba da bincike tare da gudanar da taron masu ruwa da tsaki domin hana sake faruwar irin wannan rikici, tare da yin kira ga al’umma su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai.
