
Aminu Abdullahi Ibrahim
Wani matashi ɗan bautar ƙasa mai suna Abdulkareem Abdulrasheed ya gyara tare da samar da kayan aiki a wani aji da ya daɗe babu amfani da shi a makarantar Government Day Secondary School da ke Kofai, a ƙaramar hukumar Ardo-Kola ta jihar Taraba.
Matashin ya gudanar da aikin ne ƙarƙashin wani shiri mai taken Hope Sits in Classroom, domin inganta yanayin koyarwa da karatu da kuma samar wa ɗalibai ingantattun wuraren zama.
Kafin aikin, ajin na cikin mummunan yanayi, inda bangonsa ya tsage, rufin ajin ke zubar da ruwa, da rashin sili.

Abdulrasheed ya ce abin da ya ja hankalinsa shi ne ganin wasu ɗalibai suna tsayawa yayin darasi, yayin da wasu ke zama a kan tagogi saboda ƙarancin kujeru da ajujuwa.
Ya bayyana cewa aikin ya haɗa da gyaran ajin da samar da kujeru da tebura 25, allo.
Ana sa ran aikin zai amfani ɗalibai sama da 100 a kowane zangon karatu, tare da amfanar da fiye da ɗalibai dubu ɗaya nan gaba, da kuma malamai sama da 11.

An gudanar da aikin ne tare da tallafin ƙungiyar agaji ta NaijaSolve da ke Legas, ƙarƙashin shirin NYSC Impact Challenge, inda ƙungiyar ta ɗauki nauyin kashi 80 cikin 100 na kuɗin aikin, yayin da ɗan bautar ƙasar da makarantar da al’ummar yankin suka haɗa kai wajen samar da ragowar kashi 20 cikin 100.
An fara aikin a watan Satumban 2026, kuma aka kammala shi a watan Oktoba, inda jami’an hukumar bautar ƙasa NYSC a jihar Taraba suka ƙaddamar da shi a hukumance.
Abdulrasheed, wanda ya fito daga Ilorin ta jihar Kwara, ya kammala karatunsa a Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, inda ya samu digirin farko mai daraja ta musamman a fannin ilimin halittar tsirrai da dabbobi, wato Education Biology.
