Sanatan Bauchi ta Kudu, Shehu Buba Umar, ya ce ya shirya fuskantar shari’a idan jami’an tsaro suka gano cewa yana da hannu a wasu daga cikin zarge-zargen da ake yi masa na alaka da ’yan bindiga, daukar nauyin ta’addanci da satar mutane.
Sanatan ya bayyana hakan ne a Bauchi yayin da yake mayar da martani kan zarge-zargen da aka dade ana yadawa a kansa. Ya musanta zargin, yana mai cewa bai aikata laifin da ake danganta shi da shi ba.
Shehu Buba, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin kiwon dabbobi, ya ce ya mika kansa ga hukumomin tsaro domin a gudanar da bincike mai zaman kansa.
Ya ce baya son a karbi musantawarsa kawai, yana mai bukatar hukumomin tsaro su binciki lamarin su gano gaskiyar abin da ya faru.
“Ba ni da abin boyewa, kuma ba ni da abin tsoro,” in ji shi, yana mai cewa a gurfanar da shi idan aka samu hujjar da ta tabbatar da aikata laifi.
Sanatan, wanda shi ne dan takarar gwamnan Bauchi na jam’iyyar PRP a zaben 2027, ya kuma ce wasu daga cikin alakarsa da jami’an tsaro a baya sun kasance ne saboda aikinsa na majalisar dattawa da kuma kokarin yaki da ta’addanci, satar mutane da sauran manyan laifuka
