Shugabannin Jam’iyyar NNPP na mazaɓar Gargari da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun sanar da korar Shugaban jam’iyyar na jihar, Dr. Hashimu Sulaiman Dungurawa.
Sanarwar ta fito ne ta bakin Shugaban jam’iyyar na mazaɓar, Shu’aibu Hassan, yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a yankin.
Shu’aibu Hassan ya bayyana cewa sun ɗauki matakin ne bisa zargin cewa Dr. Dungurawa na haddasa rikici a cikin jam’iyyar, tare da korar wasu muhimman ’ya’yan jam’iyya ba tare da bin ƙa’ida ba.
Haka kuma, sun zarge shi da zagin Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf.
Shugabannin mazaɓar sun kuma ce ana zargin shugaban jam’iyyar na jihar da ƙin halartar tarukan masu ruwa da tsaki a matakin ƙaramar hukuma, lamarin da suka ce na kawo cikas ga haɗin kai da cigaban jam’iyyar a yankin.
Shugabannin Jam’iyyar sun ce matakin korar ya zama dole domin kare martaba, tsari da mutuncin Jam’iyyar NNPP.
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar NNPP ke fuskantar rikicin cikin gida, musamman a daidai lokacin da ake ta yaɗa raɗe-raɗin yiwuwar sauya sheƙar Gwamnan Jihar Kano zuwa Jam’iyyar APC.
