
Guda cikin ƴan takarar neman kujerar shugabancin ƙasar Kamaru ya yi ikirarin lashe zaɓen ƙasar
Issa Tchiroma Bakary wanda ke kan gaba a bayanan alkaluman zabe na bayan fage ya yi ikirarin lashe zaɓen ƙasar inda ya yi kira ga shugaba mai ci Paul Biya da ya amsa shan kaye tare da girmama zaɓin jama’ar ƙasar.
Dan takarar daga jam’iyyar adawa ya bayyana hakan ne a wani saƙon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, a tsakar daren Litinin.
Mista Bakary ya gode wa al’ummar Kamaru kan ”yarda da samar da canji” da ya ce sun yi a ƙasar. Sannan ya kuma yi alƙawarin wallafa cikakken sakamakon zaɓukan daga rumfunan zaɓen ƙasar.
Wanda ya nuna cewa shi ya lashe babban zaben na ranar 12 ga watan Oktoba.
Iƙirarin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar zaɓen ƙasar ke ci gaba da tattara sakamakon zaɓukan.
Kawo yanzu hukumomin Kamaru ba su ce komai ba game da iƙirarin jagorar adawar, to amma a baya ministan cikin gida na ƙasar, Paul Atanga Nji ya nanata haramcin iƙirarin nasara daga ɗaiɗaikun ƴantakara tare da wallafa abin da ya kira haramtaccen sakamakon zaɓe.
Jinkirin bayyan sakamakon da wasu ke zargin kokarin murdiya ya haifar da tashe-tashen hankula a wasu manyan garuruwan kasar ciki har da Garou da kuma Yaounde a inda aka yi kone-kone.
Bakary shi da wasu ‘yan takara na fafatawa ne da shugaba ma ci Mista Paul Biya wanda ke rike da ragamar mulkin kasar sama da shekara 40, inda yake neman yin tazarce na wasu shekaru 7 a wannan zaben.