Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Shisu Adam, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Dutse ranar Alhamis, ya ce ƙungiyar ta ƙware wajen satar babura, karɓar kayan sata da kuma aikata wasu laifukan tashin hankali a jihohin uku.
A cewar rundunar, binciken ya samo asali ne bayan wani daga cikin waɗanda ake zargin ya kai hari ga wani mai babur haya a yankin Aujara, da ke ƙaramar hukumar Jahun, inda ya kwace masa babur, jami’an ’yan sanda tare da taimakon ’yan sa-kai sun mayar da martani, suka kwato babur ɗin tare da kama wanda ake zargin.
Rundunar ta ce yayin gudanar da bincike na sirri, waɗanda aka kama sun bayyana hannu a satar babura akalla 33 a wurare daban-daban, haka kuma, an ce sun amsa zargin hannu a hare-haren tashin hankali da suka jikkata wasu mutane, da kuma kashe mutane tara a jihohin Jigawa, Kano da Kaduna.
Daga cikin waɗanda rundunar ta bayyana sunayensu akwai Ado Saleh, wanda aka fi sani da Datti, Abdullahi Saidu, Magaji Danladi, Sabiu Miko, Habibu Dan Iya, Shamsu Sani, Ali Salisu, Alhassan Isa da Ado Ali.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Tijjani Murtala, ya umarci sashen binciken manyan laifuka na SCID da ya ci gaba da bincike domin gano sauran mambobin ƙungiyar, kwato ƙarin babura da kuma tabbatar da kisan da ake zargi.
