Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya taya takwaransa na jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, murnar rantsar da shi domin ci gaba da mulki a wa’adi na biyu.
Gwamnan wanda mataimakinsa, Murtala Sule Garo, ya wakilta ya bayyana rantsar da Oyebanji a matsayin muhimmin mataki a rayuwarsa ta siyasa, wanda ke nuna irin amincewar da al’ummar jihar Ekiti suka yi da jagorancinsa.
Gwamnan ya yi fatan wa’adin na biyu zai ba Oyebanji damar ƙarfafa nasarorin da ya samu a baya, inganta tsarin dimokuraɗiyya da kuma hanzarta ayyukan ci gaba a faɗin jihar.
Ya kuma buƙaci gwamnan da ya ci gaba da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da suka shafi bukatun al’umma, tabbatar da shugabanci mai haɗa kowa da kowa, tare da inganta rayuwar jama’a.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Abba na jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin gwamnatocin jihohi wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa, bunƙasa tattalin arziki da tabbatar da ci gaba mai ɗorewa, tare da yiwa Gwamna Biodun Oyebanji da mataimakiyarsa, Monisade Afuye, fatan samun nasara a mulkin su.
