Hukumar zaɓe ta kasa ta ce ta sake samun buƙatu daga ƙungiyoyi 12 domin yi musu rajistar zama jam’iyyun siyasa.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na X ta ce tuni aka shigar da buƙatun jam’iyyun cikin jerin waɗanda ke jiran layin samun rajistar hukumar.
A makon da ya gabata ne shugaban hukumar zaɓen Farfesa Mahmud Yakubu ya ce INEC ta samu buƙatu daga ƙungiyoyi 110 da ke son yi musu rajistar zama jam’iyyun siyasa.
Hukumar ta ce za ta duba waɗannan buƙatu, domin ganin ko sun cika ƙa’idojin da hukumar ta gindaya.
Yanzu dai Najeriya na da jam’iyyun siyasa aƙalla 18, kuma idan duka waɗannan ƙungiyoyi suka samu rajista adadin jam’iyyun siyasar ƙasar ka iya kai wa 140.
