Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta kasa reshen jahar Kano ta sanar da fara rijistar katin zaɓe a dukkan mazabu 12 na Karamar Hukumar Dala daga 2 ga Fabrairu zuwa 12 ga Afrilu, 2026.
Shugaban Hukumar zabe na yankin Dala, Alhaji A. A. Maulud ne bayyana hakan yayin taron masu ruwa da tsaki kan harkokin zaɓe.
Ya ce rijistar ta shafi sabbin masu jefa ƙuri’a masu shekaru 18 zuwa sama, da kuma waɗanda katinsu ya lalace, ko aka samu kuskure a bayanai, ko masu son canja wurin yin zaɓe.
- INEC za ta gana bangarorin dake rikici a jam’iyyar ta PDP
- Shugaban INEC Ya Mika Ragamar Hukumar ga Shugabar riko
Ya jaddada cewa ba za a yi wa duk wanda bai kai shekaru 18 rijista ba, tare da kira ga jama’a da su fito su yi rijista ko su gyara bayanansu.
Ya kuma bayyana cewa ana iya fara rijista ta yanar gizo, amma dole ne a kammala ta a ofishin zaben.
