Hukumar yaki da cin hanci ta (ICPC) ta sanar da kwato wasu kayan aiki da ake zargin za a iya amfani dashi wajen sauraron tattaunawar wayar tarho a gidan tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir el-Rufai, da ke Abuja.
Hukumar ta ce ta samu umarnin Kotun Majistare da ke Bwari a Babban Birnin Tarayya (FCT) domin tsare el-Rufai na tsawon kwanaki 14, wanda wa’adinsa zai ƙare a ranar Alhamis.
Haka kuma, hukumar ta roƙi Babbar Kotun Bwari dake Abuja da ta yi watsi da ƙarar da el-Rufai ya shigar, wadda ke zargin tauye masa ’yancinsa na ɗan Adam.
ICPC ta ce tsohon gwamnan na da zarge-zargen cin hanci da rashawa da ya kamata ya amsa, ciki har da tambayoyi kan inda Yuro miliyan daya da dubu 400 suka shiga; da kuma tura wasu kuɗi zuwa asusun da ba a bayyana ba har N428,122,180.18, da sauransu.
Hukumar ta kuma tabbatar da cewa wani mataimaki na tsohon gwamnan, wanda ake zargin yana da alaƙa da lamarin, ya fice daga ƙasar.
Hukumar ta ce dukkan kayan da ake zargi, an kwato su ne a gaban matar tsohon gwamnan, Hadiza Isma el-Rufai, da ɗansa, Hon. Bello el-Rufai.
ICPC ta kuma zargi tsohon gwamnan da ƙin ba da haɗin kai ga masu bincike, inda ta ce ya zaɓi yin shiru har sai an kai shi gaban kotu. Ta ƙara da cewa wani mataimaki da ke da alaƙa da binciken ya tsere daga ƙasar.
