
Aminu Abdullahi Ibrahim
Mazauna unguwar Rimin Auzinawa da ke Tudun Yola C a ƙaramar hukumar Ungogo, Jihar Kano, sun roƙi Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya shiga tsakani kan abin da suka bayyana a matsayin barazana ga tsaron al’umma sakamakon zargin rufe wata hanyar jama’a ba bisa ƙa’ida ba.
Da yake magana da manema labarai a ranar Litinin, lauyan al’ummar, Barrista Aminu Garba Sabonsara, ya ce rikicin ya samo asali ne daga zargin da ake yi wa wani mazaunin unguwar, Magaji Isyaka Mai Hula, da mayar da hanyar jama’a tamkar mallakarsa ta kashin kansa, inda ya sanya ƙofa mai ƙarfi tare da hana sauran mazauna amfani da ita.
Lauyan ya bayyana cewa tun farko al’ummar sun amince da sanya ƙofofin tsaro a mashigai saboda matsalar rashin tsaro, kuma Magaji Mai Hula ya yi alƙawarin samar da ɗaya daga cikin ƙofofin.
Sai dai, a cewarsa, bayan an girka ƙofar, Mai Hula ya sauya makullinta, ya hana sauran mazauna shiga ta hanyar, tare da ikirarin cewa hanyar mallakarsa ce.
Barrista Sabonsara ya ce wannan mataki ya haifar da damuwa da barazanar tsaro, inda mazaunan ke zargin cewa ana shigar da wasu mutane da ba a san ko su waye ba cikin unguwar ta wannan hanya da daddare.
Ya ƙara da cewa rufe hanyar ya hana jama’a zirga-zirga cikin ‘yanci, ya kawo cikas ga motocin agajin gaggawa, tare da jefa al’umma cikin haɗarin tsaro.
A cewarsa, an kai ƙorafin gaban Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (AIG) na shiyya ta daya da ke Kano, inda bangarorin suka cimma yarjejeniya a ranar 15 ga Yuni, 2026.
Yarjejeniyar ta tanadi cewa Mai Hula zai cire ƙofar ƙarfe, ya mayar da tsohuwar ƙofar da ake iya gani ta cikinta tsakanin 16 zuwa 22 ga Yuni, ya bai wa jami’an sintirin al’umma makulli, sannan a riƙa buɗe ƙofar da ƙarfe 7:00 na safe tare da rufewa da ƙarfe 10:00 na dare a kowace rana.
Sai dai lauyan ya zargi Mai Hula da gaza cika alƙawarin da ya ɗauka.
Maimakon haka, ya ce Mai Hula ya shigar da ƙara a Kotun Majistare da ke Nomansland kan wasu daga cikin mazauna unguwar yana zargin sun yi masa barazanar kashe shi.
Sabonsara ya kuma yi zargin cewa duk da umarnin kotu na hana kama ko tsare kowa yayin binciken ‘yan sanda na sashen binciken manyan laifuka na Jihar Kano (SCID) sun kama tare da tsare Ibrahim Lawal Musa, ɗaya daga cikin mazauna yankin, kafin daga bisani a sake shi bayan sa hannun kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano.

Lauyan ya roƙi Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya ba da umarnin buɗe hanyar jama’ar nan take, a tabbatar an aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a ofishin AIG, tare da gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Ya ce mazauna unguwar na ci gaba da goyon bayan warware rikicin cikin lumana, amma ya yi gargaɗin cewa ci gaba da rashin ɗaukar mataki na iya ƙara tayar da hankali a yankin.
Sai dai da muka tuntubi Magaji Isyaka Mai Hula, ya musanta dukkan zarge-zargen, yana mai cewa an raba iyakar hanyar da filinsa tun da farko. Ya kuma zargi mazauna unguwar da yi masa hassada saboda arzikinsa, yana mai cewa bai aikata wani laifi ba.
