Hukumar kwastam ta kama wani jirgin ruwan ƙasar Brazil, a tashar jirgin ruwa ta Legas ɗauke da hodar iblis mai nauyin kilogiram 25.5.
A cewar Kwastam an ɗaure ƙwayar ne a cikin wasu ƙunshi guda 24 kuma an sanya su a cikin jakunkuna biyar da aka ɓoye a cikin jirgin.
Shugaban hukumar kwastam na yankin, kwanturola Emmanuel Oshoba, ya ce jami’an leƙen asirin hukumar ne suka kai samamen tare da haɗin gwiwar hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA.
A cewar Oshoba, bayanan sirri da aka samu sun nuna cewa, bayan da jirgin ya tashi daga Brazil, ya tsaya a Honduras da Guatemala da wasu wuraren da aka san su da fataucin miyagun ƙwayoyi.
Yayin da yake mika wa hukumar ta NDLEA ƙwayar da aka kama domin gudanar da bincike, Oshoba ya sanar da cewa an tsare jirgin.
