Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta cafke ƴan mata 8 da namiji 1 bisa zargin yawon banza a wani sumame da ta yi a wasu unguwanni da manyan tituna a faɗin jihar.
Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah na Kano kan ayyuka, Dr. Mujahid Aminuddeen, ne ya bayyana hakan ga Arewa Updates.
- Hisbah za ta fara hukunta mata ƴan kasuwa da ke yin shigar banza
- Gwamnatin Kano ta haramta kafa wata Hisbah a jihar
- Hisbah sun gano gidajen aikata badala a Ja’en da kuma Gaida
Ya ce an cafke mutanen ne yayin sumamen da aka gudanar a yankunan titin zuwa Gidan Zoo, Banana Zoo Road, Ahmadu Bello Way, Lamido Crescent Way, Tukur Road Nasarawa GRA, Lodge Road Nasarawa GRA, titin zuwa Asibitin Nasarawa, Magajin Rumfa Road, Sultan Road Nasarawa GRA da Audu Bako Way.
Dr. Mujahid Aminuddeen ya ƙara da cewa a halin yanzu ana ci gaba da bincike a kan waɗanda aka cafke domin ɗaukar matakin da ya dace bisa tanadin doka.
