Babban hafsan sojin ƙasa ta Najeriya, Laftanar-janar Waidi Shaibu, ya ce rundunar sojin za ta haɗa-kai da gwamnatin jihar Taraba don ganin an tsaurara yaƙi da ta’addanci da kuma sauran matsalolin tsaro.
Laftanar-janar Shaibu ya bayyana haka ne a yau Talata, 27 ga watan Janairun, 2026 lokacin da ya karɓi bakuncin gwamnan jihar Taraba, Kanal Agbu Kefas mai ritaya a shalkwatar tsaron ƙasar da ke Abuja.
Babban hafsan sojojin ƙasar ya ce rundunar na cike da zimmar ganin sun taimaka a kowane ɓangare domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
-
An sassauta dokar hana zirga-zirga a wasu yankunan jihar Taraba
- ‘Ƴansandan bogi ɗauke da lodin tabar wiwi sun shiga hannu a Taraba
Ya yaba wa gwamnan jihar bisa irin gudummawar da yake bai wa hukumomin tsaro, inda ya ce samarwa jami’an tsaro kayan aikin da ya kamata ya janyo sojoji ƙara ƙaimi a yaƙi da suke yi da ƴan ta’adda a yankin.
Laftanar-janar Waidi ya kuma buƙaci al’umma a faɗin jihar da su cigaba da mara wa jami’an tsaro ta hanyar ba su bayanai da suka kamata wajen kama masu ta da zaune tsaye.
A martaninsa, gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas ya yaba wa sojojin Najeriya kan irin jajircewarsu wajen samar da tsaro a jihar.
