’Yan sandan osun sun kama ɗan majalisa tare da wasu mutane 146 da ake zargin ’yan daba ne
Rundunar ’yan sandan Jihar Osun ta tabbatar da kama wani ɗan majalisar dokokin jihar, Abiola Inaolaji, tare da wasu mutane 146 da ake zargin ’yan daba ne.
Rahotanni sun ce an kama mutanen ne a Ikire, da ke ƙaramar Hukumar Irewole ta Jihar Osun, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen zaɓen jihar na 2026.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Abiosun Ojelabi, ya tabbatar da kamen a ranar Asabar a Osogbo.
Ya ce an kama ɗan majalisar, wanda ke jam’iyyar Accord, ne da sanyin safiyar Asabar, yayin wani samame da Hukumar FBI ta Amurka da tawagar Intelligence Response Team, IRT, suka gudanar.
Har yanzu dai ana ci gaba da bincike kan lamarin, yayin da hukumomin tsaro ke ƙoƙarin gano dalilin kasancewar mutanen 146 a wurin da kuma abin da ake zarginsu da shiryawa.
Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara ɗaukar matakan tsaro gabanin zaɓen Osun na 2026, domin dakile duk wani yunƙuri na tada zaune tsaye ko amfani da ’yan daba wajen kan harkokin zaɓe.
