Gidauniyar Kannywood ta bayyana alhininta ga ‘yan kasuwar Singa dangane da gobarar da ta tashi a kasuwar a karshen mako.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da gidauniyar ta fitar a ranar Litinin.
“Gobarar ta haddasa asarar dukiyoyi da kayayyaki da darajarsu ya kai na miliyoyin naira. Wannan lamari shi ne karo na biyu da gobara ta tashi a kasuwar cikin ‘yan makonni, lamarin da Gidauniyar ta bayyana a matsayin abin takaici.
Gidauniyar Kannywood ta yi addu’a ga ‘yan kasuwar da suka yi hasara da kuma iyalansu wadanda suka rasu a gobarar.
Ta kuma roki Allah Madaukakin Sarki da Ya jikansu, Ya ba wa iyalansu hakuri, tare da addu’ar Allah Ya mayarwa da ‘yan kasuwar da alheri bisa asarar da suka yi.
