Gwamnatin tarayya ta ce za ta biya likitoci basussukan da suke bi, sannan za a ɗauki sababbin likitoci domin magance matsalolin da suke yawan jefa likitocin cikin yajin aiki.
Karamin Ministan lafiya Dakta Iziaq Salako ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce shugaba Bola Tinubu ya amince da fitar da kuɗin domin fara biyan likitocin nan bada jimawa ba.
Ya ce gwamnati za ta biya naira biliyan 11.9 a cikin kwana biyu domin biyan basussukan albashi da alawus-alawus da ma’aikatan asibiti ke bi.
Ministan ya ce gwamnati ta fitar da naira biliyan 10 a watan Agusta domin a fara biyan cikon albashin ma’aikatan na wata bakwai bayan ƙarin kashi 25 zuwa 35 da aka yi wa ma’aikatan lafiya na ƙasa a baya.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin ta amince a ɗauki ƙarin likitoci a wanda ministan ya ce hakan zai rage yawan aikin da likitocin suke yi.
