Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada kudurinta na kammala manyan hanyoyin tarayya a Jihar Katsina cikin lokaci, tare da tabbatar wa al’umma ingantattun hanyoyi.
Wannan tabbaci ya fito ne a yayin rangadin kafafen yada labarai na kasa kan ayyukan hanyoyi da ake yi da wadanda aka kammala a jihar, a karkashin Ajandar Renewed Hope ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Mai kula da ayyukan gini na tarayya a Katsina, Injiniya Idris Matinja, ya ce aikin hanyar Ungwan Iliya Bagudu–Kwantakaran–Tsiga–Bakori da gadojin Kadabo, na tafiya yadda ya kamata.
Ya kara da cewa aikin hanyar mai tsawon kilomita 17, da aka bayar a watan Fabrairu 2025, ya kai sama da kashi 11 cikin dari na kammalawa, tare da gina magudanan ruwa da shimfida harsashin hanya.
Injiniya Matinja ya tabbatar da cewa dukkan ayyukan na gudana bisa ka’idoji da ingantattun sharuddan Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya.
