Gwamnatin Tarayya tare da hadin gwiwar Bankin Raya Kasashen Musulmi, sun kafa sabuwar makarantar koyarwa ta harsuna a Jihar Kano domin bunkasa ilimi da hadin kan al’umma.
Karamin Ministan Ilimi, Farfesa Suwaiba Sa’id Ahmad, ta ce shirin na daga cikin Ajandar Renewed Hope ta Shugaba Bola Tinubu, wadda ke da nufin fadada ilimi mai inganci ga al’ummomin da ke bukatar tallafi.
- Gwamnatin tarayya ta sha alwashin kammala aikin manyan hanyoyi a Katsina
- Gwamnatin Kano ta kaddamar da feshin maganin sauro a wasu unguwanni
Ta bayyana hakan ne a wajen kaddamar da makarantar da ke Karamar Hukumar Kiru, inda ta ce tsarin koyarwa ta harsuna zai hada ilimin addini da na zamani.
Makarantar na daga cikin shirin Bilingual Education Project da IsDB ke daukar nauyi, wanda zai gina makarantu 30 a jihohi tara, yayin da Kano ke da guda hudu.
Gwamnati ta bukaci shugabannin makarantar da al’ummar yankin su kula da makarantar yadda ya kamata domin ta amfani dalibai da al’umma baki daya.
