Gwamnatin ƙasar Syria ta sanar da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da rundunar Syrian Democratic Forces (SDF) wadda Kurdawa ke jagoranta, bayan kwanaki da aka shafe ana fafatawa da juna a yankunan arewa maso gabashin ƙasar.
Rahotannin kafafen yaɗa labaran gwamnati sun bayyana cewa yarjejeniyar, wadda aka cimma ranar Lahadi, ta tanadi janyewar dakarun SDF daga yankunan da ke yammacin kogin Euphrates, tare da haɗe rundunar SDF cikin sojojin ƙasar Syria.
Yarjejeniyar ta biyo bayan munanan faɗace-faɗace da suka auku tsakanin sojojin gwamnati da SDF kan muƙaman soja da filayen hkar mai da ke bakin kogin Euphrates.
Da yake magana a birnin Damascus, Shugaban Ƙasar Syria, Ahmed al-Sharaa, ya bayyana cewa yarjejeniyar za ta bai wa hukumomin gwamnati damar karɓar iko a jihohi uku na gabas da arewa waɗanda a baya SDF ke riƙe da su.
Shugaban ya kuma yi kira ga ƙabilun Larabawa da ke yankunan da abin ya shafa da su kasance masu natsuwa, tare da bai wa hukumomi dama su aiwatar da dukkan sharuddan yarjejeniyar.
A cewar yarjejeniyar, hukumomin SDF da ke kula da fursunonin ISIS da sansanoninsu, tare da dakarun da ke tsaron wuraren, za a haɗa su cikin tsarin gwamnati, abin da zai bai wa gwamnatin Syria cikakken iko da alhakin tsaro da doka a wuraren.
