Hukumar Kwashe Shara ta jihar Kano, REMASAB ta kaddamar da aikin feshin maganin sauro da kwari a unguwar Tudun Yola da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a birnin Kano.
Da yake jawabi yayin aikin, Shugaban hukumar Dr Muhammad SKhalil ya ce shirin na daga cikin ƙoƙarin hukumar na tabbatar da tsaftataccen muhalli da kare lafiyar al’ummar Jihar Kano.
Ya bayyana cewa REMASAB za ta ci gaba da aikin feshin maganin sauro a faɗin kano domin dakile cututtukan da sauro da sauran kwari ke haddasawa.
Shugaban ya ƙara da cewa hukumar na ci gaba da ayyukan kwashe shara da tattara datti a tituna da unguwanni daban-daban a fadin jihar.
Dr Khalil ya kuma yaba wa Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa kokarin da yake yi wajen inganta rayuwar al’ummar jihar.
