Gwamnatin Kano ta shirya taron horaswa na kwanaki biyu ga jami’an yaɗa labaran ƙananan hukumomi 44 dake jihar, a wani ɓangare na ƙoƙarin na ƙarfafa karfafa kwazo da inganta ƙwarewar aikin jami’an a harkar sarrafa bayanan gwamnati.
Taron, wanda aka yiwa take da kare ka’idoji da kwarewar aiki kan rawar da jami’an yaɗa labaran suke takawa a fannin ingantawa da bunƙasa yaɗa sahihan bayanai ga al’umma.
Da yake ƙaddamar da taron, Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda Sakataren Gwamnatin kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim ya wakilta, ya jaddada ƙudurin gwamnati na tabbatar da gaskiya, rikon amana da ingantacciyar sadarwa, wanda ya ce horar da jami’an kan aikin su zai taimaka wajen tabbatar da shugabanci nagari.
A nasa jawabin, Kwamishinan yaɗa labaran kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya jaddada buƙatar ƙwarewa da daidaito a wajen isar da sakon gwamnati ga jama’a, tare da buƙatar mahalarta taron da su kiyaye ƙa’idoji da dabi’un al’ummar da suke rayuwa a cikin su yayin gudanar da ayyukansu.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Sakataren Gwamnatin kano Alhaji Umar Faruk Ibrahim na bayyana horaswar a matsayin wadda ta zo akan lokaci, la’akari da muhimmiyar rawar da jami’an yaɗa labaran ke takawa wajen isar da manufofi da shirye-shiryen gwamnati ga al’umma yadda ya dace.
