Gwamnatin Kano ta gabatarwa jakadun tarayyar turai daftarin bunƙasa jihar, domin ƙarfafa ci gaba mai ɗorewa, jawo hankalin masu zuba hannun jari da haɓaka haɗin gwiwar ci gaba da ƙasashen duniya.
Mataimakin Gwamna Murtala Sule Garo, wanda ya wakilci Gwamna Abba Kabir, ya bayyana cewa gwamnati ta himmatu wajen mayar da Kano cibiyar zamani mai ƙarfi ta fuskar tattalin arzikida inganta tsare-tsaren sabunta ababen more rayuwa, kare muhalli da tabbatar da ci gaba mai anfani ga kowa.
A cewar Garo Shirin bunƙasa biranen ya ƙunshi magance manyan ƙalubalen da ke tattare da haɓakar yawan jama’a, ƙarancin gidaje, sufuri, sarrafa shara, daƙile illolin sauyin yanayi da kuma samar da muhimman ayyuka ga jama’a.
Garo ya ce shirin ya yi daidai da manufofin ci gaba mai ɗorewa na duniya wato SDGs, bisa la’akari da buƙatu da muradun al’ummar Kano, inda ya ce tsarin wata hanya da gwamnati ta tsara domin jagorantar zuba jari a fannonin ababen more rayuwa, bunƙasa tattalin arziki da walwalar al’umma.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa a nasu ɓangaren, jakadun tarayyar turai ƙarƙashin jagorancin Jakadan EU a Najeriya, Ambasada Gautier Mignot, sun yabawa gwamnatin Kano kan yadda take tafiyar da harkokin tsara birane da ci gaba mai ɗorewa, tare da nuna sha’awar yin haɗin gwiwa wajen aiwatar da shirin domin inganta rayuwar al’ummar Kano.
