
Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnatin jihar Kano da jamhuriyar Guinea Bissau, sun kulla hulda kan ayyukan noma, ilimi, al’adu, yawon bude ido, da cigaban al’umma.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Alhamis.
Wannan ya biyo bayan wani babban taro da aka gudanar a birnin Guinea Bissau, inda tawagar jihar Kano karkashin jagorancin shugaban jam’iyar NNPP na kasa, Dr. Ajuji Ahmed, ta kai ziyarar ban girma ga shugaban kasar Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embaló.
Tawagar ta wakilci gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
A yayin ganawar, bangarorin biyu sun jaddada aniyarsu na karfafa hadin gwiwa a fannonin samar da ayyukan yi, da karfafa gwiwar matasa.
Haɗin gwiwar zai shafi koyar da gyaran waya, kiwon kifi, da sarƙoƙi na cashew da mango, waɗanda ke da mahimmanci don haɓaka tattalin arziki da samar da ayyukan yi.
A wani bangare na yarjejeniyar, gwamnatin jihar Kano ta ba ‘yan kasar Guinea Bissau guraben karo karatu har guda 50 don yin karatun Turanci da Hausa a daya daga cikin manyan makarantu mallakar gwamnati.
Shirin na nufin samar da musayar al’adu da harshe tsakanin gwamnatocin kasashen biyu da kuma karfafa alakar tarihi tsakanin kasashen yammacin Afirka.
A nasa jawabin, shugaban kasa Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embaló, ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa yadda yake jagoranci tare da bayyana aniyarsa ta kawo ziyara Kano.
Ya bayyana cewa tuni ya umurci ministan tsaron sa da ya jagoranci tawagar gwamnati zuwa jihar Kano domin lalubo hanyoyin hadin gwiwa.
Tawagar jihar Kano ta hada da Amina Abdullahi, kwamishiniyar harkokin mata, yara da nakasassu, Sadiya Abdu Bichi, mai ba da shawara ta musamman kan mata, yara da nakasassu, Arc. Danjuma Zarewa, tsohon Darakta-Janar na Kawata Birane; da Hon. Muhammad Sani Gumel.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada aniyar gwamnatinsa na kulla kawance da kasashen Ketare domin samar da damarmmaki ga al’ummar Kano, musamman ta fuskar ciyar da dan Adam gaba da kasuwanci da musayar al’adu.