
Gwamnatin za ta yi aikin ne a unguwannin Bulbula da Gayawa a hukumomin Ungogo da Nassarawa na jihar.
Kwamishinan Kula da Muhalli da Sauyin Yanayi Dakta. Dahir Hashim, ya bayyana cewa an ba da aikin ne ga kamfanin Habib Engineering kan kudin Naira biliyan 8,497,595,290, kuma za a kammala shi cikin kwanaki 715 a yayin bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar kwangilar a ranar Laraba.
“Wannan aikin babban mataki ne wajen kare rayuka da hanyoyin samun abinci na al’ummar Bulbula da Gayawa, waɗanda ambaliyar kwazazzabai ta addaba na tsawon shekaru.”
“Unguwannin biyu sun daɗe suna fuskantar matsananciyar zaizayar ƙasa, da ta haifar musu da asarar rayuka da dukiyoyi ba tare da gwammnati ta kai musu ɗauki ba.” in ji kwamishinan kuma shugaban shirin ACRESAL.
Kwamishinan ya kuma yaba wa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa kawo ɗauki ga waɗannan yankuna da su ka kwashe sama da shekaru 20 a halin ƙaƙanikayi sakamakon zaizayar ƙasa.
Ya tabbatar da cewa za a kammala aikin akan lokaci kuma al’ummar yankuna za su samu ci gaban tattalin arziki sakamakon bunƙasar sana’o’insu da za a samu bayan aikin.